(ABNA24.com) Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Anas Sairafi shugaban kwamitin kula da harkokin gyare-gyare da ayyukan gini da ake gudanarwa a masallacin harami ya bayyana cewa, an matsa da kofar daga inda take a tsohon gini da mita kimanin 50 daga waje.
Ya kara da cewa tsawon kofar yanzu ya kai mita 51 wato an samun kimanin mita 20 a kan yadda gininta yake a baya, yayin da tsawon hasumiyarta ya kai mita 137.
Wannan dai na daga cikin sabbin ayyukan da aka gudanar a ci gaba da aikin gyaran haramin Makka mai alfarma.






342/